Amnesty ta zargi Sojin Chadi da murkushe masu zanga-zangar lumana

Kungiyar Amnesty International ta bayyana damuwa akan yadda hukumomin kasar Chadi ke take hakkin Bil Adama wajen murkushe masu zanga zangar lumana.

Kungiyar Amnesty ta hannun mai binciken ta Abdoulaye Diarra ta bayyana dakile zanga zangar da jami’an tsaro suka yi a karshen mako a matsayin ci gaba da take hakkin Dan Adam.

Kungiyar ta ce kokarin hana jama’a fitowa zanga zangar ya ci tura, saboda haka hukumomin kasar suka yi amfani da jami’an tsaro wajen mamaye titunan birnin Ndjamena da kuma harba hayaki mai sa hawaye, abinda ya yi sanadiyar raunata mutane da dama da kuma kama wasu, kafin sakin su daga bisani.

Diarra ya ce a ranar zanga zangar an dakile layukan sadarwa a wasu sassan birnin Ndjamena, abinda ke nuna rawar da hukumomin kasar ke takawa na shekaru 5.

Kungiyar ta ce akalla mutane 16 aka kashe tsakanin ranar 27 ga watan Afrilu zuwa 19 ga watan Mayun bana sakamakon kai hari akan masu zanga zanga a birnin Ndjamena, yayin da ta bukaci hukumomin kasar da su dakatar da tirsasawa masu zanga zangar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *