Za’a kashe Naira biliyan 1 da miliyan 600 don sayen motocin shugaban kasa

‘Yan Najeriya na cece-kuce dangane da shirin fadar shugaban kasar da ta ware zunzurutun kudi har naira biliyan daya da miliyan dari shida domin sayan motaoci da safayansu.

Wannan na kunshe ne a cikin kudirin kasafin kudin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar wa Majalisun kasar biyu na dattawa da kuma wakilai a zamansu na ranar Alhamis.

Yanzu haka Kasafin kudin na Naira tiriliyan 16.39 na da gibin Naira tiriliyan 6.26, wanda Ministar Kudin Zainab Ahmed, ta ce gwamnati za ta karbi karin rance don cike  gibin.

A kasafin kudin shekarar da ta gabata, an ware N436m domin sayen motocin da safayansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *