UEFA ta fi fifita aljihunta fiye da lafiyar dan wasa – Courtois

Golan Real Madrid dan asalin Belgium, Thibaut Courtois ya caccaki Hukumar Kwallon Kafar Turai ta UEFA, yana mai cewa, ta fi fifita kudi fiye da kula da lafiyar dan wasa da ake daukar sa tamkar sakago a cewarsa.

Golan ya buga dukkanin wasanni biyu da Belgium ta yi a gasar Nations League da ta gudana a baya-bayan nan kuma kusa da kusa.

Courtois ya buga wasan da suka yi da Italiya a ranar Lahadi, wasan da ya sanya shi furta kalaman caccakar ga UEFA, inda ya ce, wannan wasa na kudi kawai  kuma dole mu fadi gaskiya a cewarsa.

Golan ya kara da cewa, sun buga wasan ne kawai saboda UEFA za ta samu karin kudin shiga daga fafatawar wadda Belgium ta sha kashi a hannun Italiya da ci 2-1

Golan ya yi caccakar ce domin nuna fushinsa kan halin da dama daga cikin ‘yan wasan Belgium ke cikin na rauni, lamarin da ya sa kasar ta ajiye zaratan ‘yan wasanta irinsu Eden Hazard da Romelu Lukako.

Sun samu raunin ne  a yayin karawar da suka yi da Faransa kwanaki uku da suka gabata a matakin wasan dab da na karshe.

Kazalika Golan ya yi korafi kan yadda ake shirya musu wasanni kusa-kusa kuma akai akai ba tare da la’akari da hutunsu da lafiyarsu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *