Birtaniya za ta bai wa Faransa kudin hana kwararar baki

Birtaniya ta ce nan gaba kadan za ta bai wa Faransa wasu kudade da yawansu ya kai Euro miliyan 60 da nufin amfani da su wajen dakile kwararar bakin haure zuwa kasar.

Wannan na zuwa ne bayan da Faransar ta yi korafin cewa har yanzu ba a ba ta wadannan kudaden da tuni aka yi mata alkawarin su.

Ana dai ganin jinkirin na zuwa ne sakamakon barazanar da Sakatariyar Harkokin Cikin Gida ta Birtaniya Priti Patel ta yi ta dakatar da bai wa Faransa kudin, duk kuwa da yadda Faransar ke fama da kwararar bakin haure da ke ratsawa ta kasar zuwa Birtaniya.

Sai dai kuma Ministan Cikin Gidan Birtaniyan Damian Hinds ya ce za a biya kudin cikin makonni masu zuwa.

A nasa bangaren Ministan Cikin Gidan Faransa Gerald Dramanin ya ce, akwai bukatar shirya wata tattaunawa tsakanin Tarayyar Turai da Birtaniya kan ta’azzarar kwararar bakin hauren, wanda ya alakanta da rashin biyan kudin akan lokaci.

Akalla mutane dubu 15 da 400 ne suka yi aniyar tsallakawa wasu nahiyoyin cikin watanni 8 da suka gabata, karin kaso 50 kenan kan adadin da aka samu a bara.

A cewarsa mutanen 491 ne suka tsallaka zuwa Birtaniya daga Faransa a ranar Asabar kadai cikinsu kuma har da kananan yara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *