Bikin ranar ‘ya mace ta duniya 2021

Majalisar Dinkin Duniya ta ware kowacce ranar 11 ga watan Oktoba, don zama ranar yara Mata ta duniya, a wani yunkuri na ganin yaran Mata sun samu cikakkiyar kulawa ta fuskar Ilimi, tsaro da kuma cikakken ‘yancin kamar kowa.

Kamar kowacce shekara, bana ma asusun tallafa wa  Ilimi, kimiyya da al’adu na Majalisar Dinkin Duniya UNESCO na jagorantar bikin ranar ‘ya’ya Mata yayin da taken ranar a bana shine : ‘‘Zamani mai cike da sabbin fasahohi’’ ranar da ke da nufin karfafa gwiwa ga mata da kuma lalubo halin da suke ciki tare da magance matsalolin da suke fuskanta baya ga basu damar yin gogayya a kowanne fanni na rayuwa.

Wasu daga cikin manufofin ranar, wadda aka fara bikinta daga shekarar 1995 yayin taron mata na Duniya a Beijing, na da nufin samar da daidaito tsakanin yara Mata ta fuskar Ilimi da takwarorinsu maza tare da cimma muradan da ake fatan ganin matan sun kai don dakile koma bayan da suke fuskanta musamman a kasashe masu tasowa.

Manufar samar da daidaiton jinsi tare da karfafa gwiwar mata a dukkan matakai baya ga mayar da su masu dogaro da kansu na daga cikin kuduran da ke kunshe a muradan ci gaba 17 da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya a gaba tun daga shekarar 2015.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *