Yau kotun soji a Burkina Faso ta fara shari’ar da aka dade ana dako wa mutane 14 da ake zargin su da kashe tsohon shugaban kasa Thomas Sankara shekaru 34 da suka gabata.
Daga cikin wadanda ake tuhuma harda tsohon shugaban kasa Blaise Compaore da na hannun daman sa Janar Gilbert Diendere.
A ranar 15 ga watan Oktobar shekarar 1987 wasu bijirarun sojoji suka budewa shugaba Sankara da wasu jami’an sa 12 wuta a juyin mulkin da ya baiwa Blaise Compaore damar hawa karagar mulki.

Bayan kashe Sankara, Compaore ya kwashe shekaru 27 yana jagorancin Burkina Faso kafin boren da ya tilasta masa tserwa daga kasar a shekarar 2014 inda yayi gudun hijira zuwa Cote d’Ivoire wadda ta bashi takardar zama ‘dan kasa.
Janar Diendere dake cikin wadanda ake tuhuma yanzu haka na zaman gidan yari akan daurin shekaru 20 da aka masa saboda yunkurin juyin mulkin a shekarar 2015, kuma yau ya bayyana a gaban kotun sojin cikin damara.
Wani fitaccen jigo da ake tuhuma a shari’ar shine Hyacinthe Kafando, wanda tsohon jami’i ne a rundunar tsaron fadar shugaban kasa, amma a halin yanzu ya gudu.
Compaore ya dade yana watsi da zargin da ake masa na kashe abokin sa Sankara a juyin mulkin, yayin da lauyoyin sa suka ce ba zai gurfana a gaban kotun ba, saboda yana da kariyar tsohon shugaban kasa.
Duniya ta zuba ido ta ga yadda wannan shari’a zata kaya, musamman ‘yan Afirka dake juyayin kashe shugaban da ake yiwa kallon jagora na gari lokacin mulkin sa.