Wakilan Amurka sun gana da manyan wakilan Taliban a Qatar don tattaunawa kan sha’anin tsaro da kuma yadda za a inganta shirin kare hakkin dan adam a Afghanistan.
Aranar Asabar ne dai tawagar wakilan suka sauka a Doha babban birnin kasar Qatar, domin ganawa da manyan wakilan na gwamnatin Taliban game da sha’anin ayyukan ta’addanci da kuma yadda za kare lafiyar Amurkawa da ma sauran baki ‘yan kasashen waje da kuma ‘yan kasar ta Afghanistan.
A cewar mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, Ned Price, a zaman da bangarorin biyu suka yi sun tabo batun kare hakkin bil’adama da suka kunshi kare hakkin mata, musamman karatun yara mata da ake ganin na neman sauya akala a kasar.
Bangarorin biyu sun kuma tattauna yadda Amurka ke bayar da agajin jin kai mai karfi, kai tsaye ga jama’ar Afghanistan.
A cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, an cimma yarjejeniya a tattaunawar kuma wakilan na Amurka sun sake nanata cewa za a yi wa mulkin Taliban hukunci ne bisa abin da aka gani a kasa, ba wai abin da ta fada da baka ba.
Taliban na neman amincewar kasashen duniya, da kuma taimako musamman na jin kai, bayan da suka koma kan mulki a watan Agusta lokacin da sojojin Amurka suka fice daga kasar, bayan shekaru 20 ana yaki.