Za ka iya karban bashi don aiwatar da Kasafin Kudin 2022, Shugaban Majalisa ga Buhari

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai iya cigaba da karban basussuka saboda Najeriya na bukatar kudi yanzu.

A cewarsa, wannan shine dalilin da yasa suke amincewa duk lokacin da Shugaban kasan ya nemi izinin karban bashi.

Ahmad Lawan ya yi wannan jawabi ne lokacin da Shugaban kasa ya tafi majalisar gabatar da kasafin kudin 2022. Yace:

“Mai girma Shugaban kasa, samar da kudin shiga har yanzu babban kalubale ne ga cigaban da muke so.

“Shi yasa kwanan nan majalisa da bangaren zartaswa suka yanke shawaran a daina baiwa ma’aikatun da suke kin shigar da kudin shigan 2022 wasu kudade.”

“Shi yasa kwanan nan majalisa da bangaren zartaswa suka yanke shawaran a daina baiwa ma’aikatun da suke kin shigar da kudin shigan 2022 wasu kudade.”

“Ya kai Shugaban kasa, mun fahimci cewa sakamakon rashin kudi, ya zama wajibi gwamnati ta karbi basussuka daga gida da kasashen waje domin gudanar da ayyuka a fadin tarayya.”

“Shi yasa muke bada daman karban wadannan basussuka. Wajibi ne a cika alkawuran da aka yiwa mutane saboda haka sai an samo kudi ta ko wani hanya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.