Super Eagles ta sha kashi a Lagos

Najeriya ta sha kashi a hannun Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a karawar da suka yi na neman zuwa gasar cin kofin duniyar da za’ayi a Qatar a shekara mai zuwa.

‘Dan wasan gaba na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Karl Namnganda dake wasa a rukuni na 4 na gasar Faransa ya jefawa kasar sa kwallo daya tilo da ya baiwa kasar sa nasara akan kungiyar Super Eagles ta Najeriya a karawar da suka yi a birnin Lagos.

Namnganda wanda ba a fara wasan da shi ba, ya rufe bakin Yan kallon da suka yi tururuwa zuwa filin wasan Lagos lokacin da ya jefawa kasar kwallon da ya taimaka mata samun nasara.

Wannan nasarar ta baiwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya damar samun maki 3 daga Najeriya da kuma zama a matsayi na 3 a tebur na rukunin Ca da maki 4 kamar yadda Cape Verde ke da maki 4 a matsayi na 2, sai dai har yanzu Najeriya na da maki 6 a matsayi na farko.

Wannan rashin nasara ya yiwa ‘Yan Najeriya masu sha’awar kwallon kafa illa, musamman ganin cewar a Najeriya akayi karawar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *