Macron na taro da matasan Afrika don jin korafinsu

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa na karbar bakwancin wani taro kan Afirka a yau Juma’a, inda yake ganawa kai tsaye da matasan nahiyar domin sauraren abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya.

Maimakon sauran shuwagabannin kasashe, Macron ya yaggayaci daruruwan matasa ‘yan kasuwa, masu fasaha da kwararru kan harkokin wasanni zuwa kudancin Montpellier, birnin da ke barkar bakwancin taron.

Kamar yadda fadar shugaban kasar ta fitar da sanarwa, manufar taron ita ce, sauraren kalaman matasan Afirka da kuma neman mafita kan kalubalen da ke addabarsu.

Ganawar ta zo ne a wani lokaci mai cike da sarkakiya tsakanin Faransa da kwayayenta da suka yi mulkin mallaka a Afirka, yayin da ake takaddama kan yanke shawarar hana takardun Bisa  ga ‘yan kasashen Algeria da Morocco da Tunisia.

Algeria dai ta umarci jakadanta na Faransa ya koma gida, bayan da rahotanni suka ce Macron ya ce kasar na amfani da tsarin mulkin soja, yayin da rikici ya barke tsakanin Faransa da Mali kan shirin tura sojojin haya na Rasha a wani bangare na yaki da mayakan jihadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.