Gwamnonin Najeriya da Nijar na shirya taro akan matsalar tsaro

Wasu Gwamnonin Najeriya da suka fito daga Yankin Arewa maso Yamma na shirin gudanar da taro da takwarorin su na Jamhuriyar Nijar da suka hada iyaka domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro a tsakanin su.

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da haka bayan ya ziyarar da ya kai Jihar Maradi wadda ke dauke da daruruwan ‘Yan gudun hijirar da suka tsere daga Najeriya.

Tambuwal yace zasu gudanar da taron ne da gwamnonin jihohin Dosso da Tahwa da kuma Maradi, kuma cikin gwamnonin Najeriya da zasu halarci taron harda takwarorin sa na jihohin Zamfara da Katsina.

Gwamnan ya bayyana cewar abin takaici ne yadda matsalar rashin tsaro ta dabaibaye yankin na su, yayin da ya kara da cewa suna iya bakin kokarin su a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari domin dawo da zaman lafiya a jihohin dake kan iyakokin.

Tambuwal ya mika sakon godiya daga shugaba Buhari zuwa shugaba Bazoum Muhammad akan karimcin da suka musu na kula da dubban ‘Yan gudun hijirar da suka tsugunar daga Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *