Theo Hernendez ya cilla Faransa zuwa matakin karshe na gasar cin kofin Kasashen Turai ta Nations League bayan ya zura kwallon karshe a ragar Belgium a minti na 90 a karawar da bangarorin biyu suka yi a jiya Alhamis, inda suka tashi 3-2.
Nasarar da tawagar Faransa ta samu ta zo da mamaki, ganin yadda ta yunkuro har ta farke kwallaye 2 da Belgium ta fara zura mata, sannan daga bisani Hernendez ya kara ta uku ana gab da tashi wasan.
Hernendez mai taka leda a AC Milan, ya sha jinjina saboda yadda ya cire wa Faransa kitse a wuta, kuma a karon farko kenan da ya jefa kwallo a raga a wasan kasa da kasa.
Theo Hernendez, dan uwa ne ga Lucas Hernendez, yayin da aka hadu su tare a cikin tawagar ta Faransa a wasan na jiya.
Yanzu haka tawagar ta Faransa za ta hadu da takwararta ta Spain a wasan karshe na gasar ta Nations League a ranar Lahadi mai zuwa a filin wasa na San Siro da ke birnin Milan.