Bazoum ya gana da wakilin MDD akan yawan jama’a

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya gana da wakilin Hukumar kula da yawan jama’a na Majalisar Dinkin Duniya a Kasar Mr Ismaila Mbengue dangane da shirin wani taro da za’ayi wanda zai mayar da hankali akan batutuwan da suka shafi yaki da auran wuri da tsara iyali da kuma ci gaban ilimin yara mata.

Ana saran gudanar da taron fadakarwar ne tsakanin 21 zuwa 23 ga watan Nuwamba mai zuwa, kuma daga cikin mahalarta taron harda sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma.

Fadar shugaban Nijar tace taron zai gudana ne a matakai guda 3 da su mayar da hankali akan yadda ake aurar da yara mata da wuri da kuma yadda ya dace jama’a su tsara iyalan su dangane da yaran da suke haifa, sai kuma batun samarwa yara mata ilimi da kuma basu damar ci gaba da neman ilimi.

Gwamnatin Nijar tace taron zai baiwa sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma damar gabatar da matsayin su akan wadannan batutuwa tare da kyawawan matakan da ake dauka domin amfani da su a sassan kasa.

Sanarwar tace wannan mataki zai baiwa gwamnati da masu taimaka mata damar tsara irin matakan da zasu aiwatar wadanda zasu amfani jama’ar kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *