Spain ta kawo karshen jerin nasarorin Italiya

Spain ta taka wa Italiya birki a tafiyar da take na jerin wasannini 37 ba tare da an doke ta ba,  sakamakon kwallaye 2 da Ferran Torres ya saka a ragar Italiyar a filin wasa na San Siro a daren Laraba, a wasan kusa da karshe na gasar lig din nahiyar Turai da aka tashi 2-1.

Italiya ta buga ilahirin zubi na 2 na wasan ne da ‘yan wasa 10 sakamakon jan kati da aka bai wa kyaftin din tawagarta Leonardo Banucci, amma ta nuna jajircewa a kokarinta na kauce wa rashin nasara  a karon farko tun  a watan Satumban 2018.

Kocin tawagar Italiyar, Roberto Mancini ya ce haka wasa yake wani lokaci, yana mai cewa sun yi kuskure da bai kamace su a wannan matsayi da suke ciki.

A ranar Lahadi Spain za ta fafata  a wasan karshe da duk wadda ta yi nasara a wasa kusa da da na karshe na 2 da za a gwabza tsakanin Faransa da Belgium a wannan Alhamis.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *