Manyan PDP sun amince dan arewa ya shugabanci jam’iyyar

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar PDP a ranar Alhamis 7 ga watan Oktoba ya amince da karkatar da matsayin shugaban jam’iyyar zuwa Arewa.

Hukuncin ya biyo bayan amincewa da shawarwarin da ke kunshe cikin rahoton kwamitin karba-karba na babban taron jam’iyyar PDP na kasa wanda gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi ke jagoranta.

Kwamitin karba-karba na Ugwuanyi ya musanya shugabanci da duk wasu mukamai na zababbun jam’iyyun da mutanen Arewa ke rike da su yanzu da na Kudu.

Ya ce an umarci shugabannin jam’iyya a shiyyoyin siyasa shida da su koma sashi da kuma kananan bangarori daban-daban a zababbun mukamai tsakanin jihohi a jihohinsu daban-daban.

Bisa ga dukkan alamu, biyo bayan takaddamar da ta tarbi musanyawar yankin, Ologbondiyan ya ce NEC za ta sake ganawa a wani lokaci don duba rahoton wani kwamiti da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ke jagoranta.

Kwamitin Bala Mohammed ya ba da shawarar cewa a ba da tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023 ga duk masu bukata, ba tare da la’akari da asalin kabilar su ba.

Ologbondiyan, duk da haka, ba bayyana manufar taron NEC na nufin tattaunawa kan rahoton Bala Mohammed zai gudana ba kafin babban taron jam’iyyar na 30-31 ga Oktoba.

Taron na NEC ya samu halartar gwamnonin jam’iyyar, ‘yan majalisar kasa, tsoffin gwamnoni, tsoffin ministocin gwamnati da tsoffin shugabannin jam’iyyar.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar; shugaban kwamitin amintattu (BoT), Sanata Walid Jibrin; tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.