Mahaifiyar Mbappe ta ce danta na tattaunawar sabanta zama a PSG

Mahaifiyar shahararren dan wasan Paris Saint-Germain Kylian Mbappe ta ce batun yarjejeniyar tsawaita kwantiragi tsakanin danta da PSG din na tafiya babu kama hannun yaro duk da yadda Real Madrid ke nemansa.

Batun canza shekar Mbappe ne ya mamaye kafafen yada labarai a farkon wannan  kaka, inda daga bisani Real Madrid da ke nemansa ta hakura ganin yadda PSG ta ce ba za ta sayar da dan wasan ba.

Madrid ta yi fatan cewa dan wasan ba zai sanya hannu a wani kwantiragi da PSG ba, wato zai karkare kwantiragin don ya bar kungiyar kyauta.

Sai dai PSG ta zake cewa ba za ta sayar da shahararren dan wasanta a kan ko nawa ne ba, amma  a yayin da Madrid ke fatan cimma yarjejeniya da dan wasan  a kaka mai zuwa, PSG na kokarin rinjayarsa ya tsawaita kwantiraginsa don ya ci gaba da zama a kungiyar.

Mbappe dai ya sha bayyana aniyarsa ta komawa Real Madrid.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *