Kasar Saudiyya ta saye kungiyar kwallon kafa ta Newcastle

Kungiyar kwallon kafa mai buga Firimiya a kasar Ingila, Newcastle United ta koma hannun wata kungiyar da Saudiyya ke marawa baya, Al-Jazeera ta ruwaito.

Kungiyar ta Newcastle United ta amince da cinikin bayan wasu takardun doka sun tabbatar da cewa kasar ba za ta yi tasiri kan harkoki ko iko da kungiyar ba.

A cewar sanarwar Firimiya:

“Kungiyar Gasar Firimiya, Newcastle United Football Club da St James Holdings Limited sun warware takaddamar da ake yi kan karbe kungiyar daga hannun PIF, PCP Capital Partners da RB Sports & Media”

Rahotanni sun bayyana cewa, duk da cewa 80% cikin 100% na kudaden cinikin fam miliyan 300 da aka kulla kan kungiyar ya zo ne daga asusun ajiya na zuba hanayen jarin kasar, hakan ba zai shafi gudanar da kungiyar ba.

A yanzu dai mallakar kungiyar a hannun Saudiyya ya tsallake duk wani cike-ciken takardu tsakanin kungiyar ta firimiya da shugabanninta.

Kungiyar na shirin zama daya daga cikin kungiyoyin da suka fi kowa kudi a duniya, inda dukiyar su za ta ninka ta masu Man City ninki goma kuma kusan ta ninka ta Paris Saint-Germain sau 50, inji rahoton Daily Mail.

A halin da ake ciki, ‘yan wasan Newcastle da ma’aikata da koci sun motsa jiki a ranar Alhamis yayin da labarin sabon sauyin ke gabatowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *