Ana tuhumar wani dan kwallon Brazil da yunkurin kashe alkalin wasa

Ana tuhumar wani dan wasan kwallon kafa na n kasar Brazil da yunkurin kisa bayan ya tokari alkalin wasa a kai a yayin wani wasan gasar karamar lig ta kasar.

Dan wasan na kungiyar Sport Club Sao Paulo William Ribeiro ya kai wa alkalin wasan Rodrigo Crivellaro hari ne bayan da ya yanke hukuncin cewa dan wasan ya yi keta a wasan na ranar Litinin.

An dakatar da wasan da Club Sao Paolo din  ke fafatawa da Gurani a cikin zubi na 2, inda aka garzaya da alkalin wasan asibiti.

Daga baya an sallami alkalin wasan, a yayin da kungiyar ta garin Sao Paolo ta kori dan wasanta Ribeiro.

Kungiyar ta ce wannan lamari da ya auku a shekarar da ta ke cika shekaru 113 da wanzuwa na daya daga cikin abubuwa mafi muni  da ta taba fuskanta a tarihinta, kuma tana nazari a kan karin matakin da za ta dauka.

An sake wasan, kuma Gurani ta yi nasara 1-0.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *