Ana binciken shugaban Austria kan zargin Rashawa

An kaddamar da binciken cin hanci da rashawa a kan shugaban Austria, Sabastian Kurz inda ake tuhumar sa da bada kudade domin samun goyon bayan kafafen yada labarai.

A sanarwar da masu shigar da karar suka fitar, sun bayyana yadda aka kai samame a wurare da dama da suka hada da ma’aikatun gwamnatin domin kafa kwararan shaidu a kan wanda ake zargin, wato Kurz da kuma magoya bayansa na jam’iyar people’s Party.

Tuni ministan kudin kasar, Gernot Bluemel, ya bada tabbacin kai samamen a ma’aitakatarsa, yayin da a nata bangaren, ma’aikatar watsa labaran kasar ta kara da cewar fadar gwamnati na daga cikin wuraren da aka kai samamen.

Zalika, masu shigar da karar sun bayyana cewar bayan shi Kurz, akwai wasu daidaikun mutane 9 tare da wasu kungiyoyi 3 da ake bincika

Binciken dai ya biyo bayan magudin zaben jin ra’ayoyin jama’a ne da aka tafka a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2018 tare da yin amfani da kudin al’umma karkashin ma’aikatar kudi wajen kare muradun jam’iyarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *