An tattauna da ‘yan bindiga a Zamfara, sun sako mutane sama da 200

Gwamnatin jihar Zamfara a ranar Alhamis ta ce ta tabbatar da sakin akalla mutane 200 da ‘yan bindiga suka sace ta hanyar tattaunawa ta lumana da sauran matakan tsaro.

Mukaddashin Gwamnan Zamfara, Nasiru Magarya, ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin Taron Shugabannin Majalisar Dokokin Jihohin Najeriya, a Gusau.

Mista Magarya, wanda shine kakakin majalisar dokokin Zamfara, ya tarbi tawagar, wacce ta kai masa ziyarar jaje bisa rasuwar mahaifinsa, Mu’azu Magarya, Daily Nigerian ta ruwaito.

A baya mun kawo muku rahoton cewa, Mahaifin mai kakakin majalisar ya mutu yayin da yake hannun ‘yan bindiga.

Tawagar, a karkashin jagorancin Shugaban Taron kuma Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Abubakar Sulaiman, ta kuma kunshi shugabannin majalisar Kano, Katsina da Yobe.

Mista Magarya ya yabawa musu bisa ziyarar, ya kara da cewa kalubalen tsaro da ke damun Zamfara ya zama abin damuwa ga gwamnatin da Gwamna Bello Matawalle ke jagoranta.

Ya kuma, ya tabbatarwa da maziyarta da mutanen jihar kudirin gwamnati na magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Da yake magana kan jimamin da ya shiga kan rashin mahaifinsa, ya kuma yi godiya cewa:

“Alhamdulillah, an yi nasarar kubutar da iyalan ciki har da jaririn dan watanni uku.

“Amma abin takaici, ga mahaifin mu, Alhaji Mu’azu Magarya, lokacin sa ya zo kuma a matsayin mu na Musulmi, dukkan mu mun yi imani cewa dole ne kowane rai na da farko da karshe.

“A madadin danginmu, Gwamnatin Zamfara da Majalisar Dokoki ta Jiha, muna godiya da wannan ziyarar.

“Ina farin cikin sanar da ku cewa gwamnatin jihar ta tabbatar da sakin sama da mutane 200 da aka yi garkuwa da su ta hanyar zaman lafiya da tattaunawa, wanda gwamnatin yanzu karkashin jagorancin gwamnan jihar ta fara.”

Mista Magarya ya lura cewa mutanen da aka saki suna kan hanyarsu ta zuwa Gusau, babban birnin jihar kuma za su iso kowane lokaci daga yanzu.

Tun da farko, Shugaban Taron Kakakin Majalisa Sulaiman, ya ce sun zo ziyarar ne domin jajantawa Kakakin Majalisar Zamfara, danginsa da mutanen jihar, kan rasuwar mahaifinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *