Al’ummar Kaduna sun kalubalanci matakan gwamnati na yaki da ‘yan bindiga

Al’umma da dama a jihar Kaduna da ke Najeriya na kokawa dangane da matakan da gwamnatin jihar ta dauka na dakile aikin ‘Yan ta’adda a  jihar inda su ke ganin cewa matakan sunyi tsauri da yawa, kuma suke bukatar a sassauta.

A makon da ya gabata ne dai gwamnatin jihar ta hana hawa babura a fadin jihar har na tsawon watanni uku tare kuma katse layukan sadarwa a wasu sassan jihar.

In kai mazaunin Kaduna ne zamu so muji raayinku, ta hanyar rubutu a kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *