Jaridar Daily Trust ta ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba 6 ga watan Oktoba ya yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Jonathan, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Sai dai kuma, an lura cewa tsohon shugaban, a matsayinsa na wakilin ECOWAS na musamman a Mali, yana ta yin taro akai-akai tare da Shugaba Buhari kan kasar ta Yammacin Afirka da ke fama da rikici.
Akwai kuma rade-radin cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulkin kasar suna zawarcin Jonathan da tikitin takarar shugaban kasa na 2023. Karin bayani…