Sakateriyar gwamnatin tarayya ta kama da gobara mai tsanani

Jaridar Punch ta rahoto cewa, yanzu haka wani bangare na Sakateriyar Gwamnatin Tarayya da ke Shiyyar Makamai Uku a Abuja na ci da wuta.

Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.

An bayyana cewa wasu ababen hawa da ke cikin sakateriyar wutar ta shafe su.

An tattaro cewa jami’an hukumar kashe gobara suna wurin don kashe wutar.

Karin bayani na nan tafe..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *