A ranar Laraba, 6 ga watan Oktoba, ‘yan majalisa biyu a majalisar dokokin jihar Anambra sun sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ‘yan majalisar, Onyebuchi Offor (Mazabar Ekwusigo), da Douglas Egbuna (Mazabar Onitsha ta Arewa), sun sanar da sauya shekarsu a zauren majalisar a Awka, ranar Laraba.
Offor wanda shi ne shugaban marasa rinjaye na majalisar ya ce ya tuntubi iyalinsa da mai ba shi shawara kan shawarar da ya yanke na barin PDP zuwa APC.
Ya yi bayanin cewa ya shiga APC ne domin mazabarsa ta dandana mulkin jam’iyyar a matakin tarayya, PM News ta kuma bayyanawa.
Egbuna shima ya bayyana cewa ya koma APC ne bayan tuntuba da dama.
Kakakin majalisar, Uche Okafor, ya taya ‘yan majalisar murna tare da yi musu fatan alheri a sabuwar jam’iyyarsu.