Miyagun yan bindiga sun bude wa masallata wuta, Sun kashe aƙalla 10 a jihar Katsina

Rahotanni sun nuna cewa aƙalla masallata 10 aka kashe yayin da wasu miyagun yan bindiga suka shiga ƙauyen Yasore, ƙaramar hukumar Batsari, jihar Katsina.

Dailytrust ta rahoto cewa lamarin ya auku ne lokacin da mutanen ke tsaka da sallar Magrib yayin da yan bindigan suka buɗe musu wuta, ranar Talata.

Tuni aka gudanar da jana’izar waɗanda suka rasu da safiyar ranar Laraba, yayin da waɗanda suka ji raunuka aka kaisu asibiti. Daga ina maharan suka fito?

Rahoto ya bayyana cewa maharan sun fito ne daga wata maɓoyarsu a dajin birnin Gwari dake jihar Kaduna.

Yan bindigan, waɗanda suka farmaki ƙauyen da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, sun kuma kona gidaje da dama a garin.

5 Replies to “Miyagun yan bindiga sun bude wa masallata wuta, Sun kashe aƙalla 10 a jihar Katsina”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *