Kiwon zuma ya bunkasa arzikin Jamhuriyar Congo

Kiwon kudan-zuma na sake samun karbuwa tsakanin mutanen jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, abin da ke kara bunkasa tattalin arzikin masu sana’ar da kuma fadada kiwonta ta hanyar zamani.

Yankin Kabalo da ke arewacin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ya yi fice wajen harkokin noman zuman, wanda masana a yankin ke dora nasarar hakan kan wata kungiya mai zaman kanta a kasar Faransa wadda ta bai wa manoman horo na musamman kan kiwon zuman.

Tuni dai manoman zuman suka fara nuna faricikinsu da wannan sabon tsari na kiwon zuman a zamanance, saboda yawan ribar da suke samu idan aka kwatanta da baya.

Medard Sibangolo shugaban sashen kula da kiwon dabbobi na gundumar Kabalo ya ce, “Muna sanya idanu a zumar domin sanin abin da take ciki idan mun bude, mun ga ruwan zumar, sai mu kwashe”.

Wani manomin zumar Daniel Mbuyu ya ce, wannan sabuwar hanyar ta biya su.

“Tshouwar hanyar na da wahala saboda sai ka je daji da wuta da hayaki kafin ka kori kudan-zumar, amma yanzu muna yi a saukake mu bar kudan zumar mu kuma kwashe ruwan zumar” inji Mbuyu.

Londres Sango shi ne jami’in Hukumar Samar da Abinci da Harkokin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya a gundumar ta Kabalo kuma a cewarsa, “ Muna girbe zuman sau biyu a shekara a watan Afrilu muna samun lita 15 a kowanne tarko, amma a watan Octoba yakan kai lita 20.”

Londres ya kuma ce, nan gaba kadan Hukumar Kula da Abinci da Harkokin Noma ta Maalisar Dinkin Duniya za ta bude babban ofishin sayar da zuma a yankin, wanda hakan zai bai wa jama’a damar samun ingatacciyar zuma zalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *