Kasashen duniya za su dade kafin su murmure – IMF

Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya yi gargadin cewa, za a samu jan-kafa wajen habbakar tattalin arziki a cikin wannan shekara, a daidai lokacin da kasashen duniya ke fuskantar tsadar farashin kayayyakin masarufi da kuma tarin basuka.

Daga cikin abubuwan da IMF ya zayyana a matsayin musabbin jinkirin farfadowar tattalin arzikin da annobar Coronavirus ta tagayyara, har da ratar da ake gani tsakanin kasashen duniya mawadata da matalauta.

Koda yake shugabar IMF, Kristalina Georgieva ta ce, a halin yanzu suna sa ran tattalin arzikin zai dan habbaka a bana, amma fa kasashe matalauta za su dauki shekaru masu tsawo kafin kammala murmurewa daga illar annobar Coronavirus a cewarta.

Georgieva ta kara da  cewa, matsalar tsadar farashin kayayyakin abinci da kuma rashin daidaiton samun rigakafin Korona ta ta’azzara.

Shugabar ta IMF wadda ke gabatar da jawabi ta kafar intanet daga birnin Washington ta ce, har yanzu, duniya ta gaza matsawa gaba tun bayan fama da annobar ta Covid-19.

A mako mai zuwa ne IMF zai fitar da sabbin hasashen habbakar tattalin arziki, hasashen da ake sa ran zai nuna cewa nan da badi,  kasashe mawadata za su maido da cikakken tagomashin da suke da shi kafin barkewar Coronavirus, sabanin kasashe masu tasowa da za su dauki dogon lokacin kafin gyagijewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *