Gwamnatin Shugaba Buhari ta yi barazanar kafa dokar ta baci a wannan jihar

A ranar Laraban nan, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata iya kafa dokar ta baci a jihar Anambra idan akwai bukatar hakan, kamar yadda Tribune ta ruwaito. A cewar gwamnatin shugaba Buhari, zata ɗauki duk matakin da ya dace domin tabbatar da an gudanar da zaɓen 6 ga watan Nuwamba a jihar.

Antoni Janar, Abubakar Malami, shine ya faɗi haka yayin da yake amsa tambayoyin manema labari jim kaɗan bayan taron FEC a fadar shugaban ƙasa.

Bugu da ƙari, Malami yace ba abinda gwamnati ba zata yi ba wajen tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *