Birtaniya ta fusata Faransa kan dokar kamun kifi

Faransa ta yi kira da babbar murya game da dokar kamun kifi, tana mai mika bukatarta ga Kungiyar Tarayyar Turai ta EU da ta kara matsa lamba kan Birtaniya tare da gargadin hadin gwiwar kasashen biyu na iya fuskantar hadari.

Tsamin dangantaka tsakanin Faransa da Birtaniya da ke kara ta’azzara tun bayan ficewar Burtaniyan daga EU, bayan da Faransa ta yi barazanar katse wa tsibirin Channel lantarki, wanda Birtaniya ta dogara akai don samar da makamashi.

Birtaniya  ta ki bada lasisin kamun kifi da jiragen ruwan Faransa ke nema duk da cewa an cimma wannan yarjejeniyar  lokacin da take fafutukar ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai, lamarin da ya sa Faransa ta fusata bayan da masunta suka shiga damuwar halin da za su iya tsintar kansu.

Bisa jerin sanarwar da gwamnatin kasar ta rika fitarwa, sun nuna cewa hakurin Faransa kan batun ya kare yayin da rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu kan lamurra da dama ya kara tabarbarewa.

Firaminista Jean Castex ya shaida wa majalisar dokokin kasar cewa aikin hadin gwiwa tsakanin Faransa da Birtaniya na cikin hadari sakamakon takaddamar, kasancewar kasashen biyu suna aiki tare kan batutuwa da dama ciki kuwa har da yin kaura ba bisa doka ba, musamman a tsibirin na Channel.

Castex ya ce, ya nemi Hukumar Tarayyar Turai da ta dauki tsauraran matakai kan Birtaniyar don tabbatar da cewa, ta cika alkawuran da ta dauka karkashin sharuddan yarjejeniyar ficewarta daga EU.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *