Mai dakin Ganduje ta koma Kano bayan ta amsa tambayoyi a ofishin EFCC

Mai dakin gwamnan jihar Kano a Najeriya, Farfesa  Hafsat Ganduje, ta koma jihar bayan da hukumar yaki nda masu yi wa tattalin arziki zagon kasa ta kasar, EFCC ta gayyace ta domin amsa tambayoyi bisa korafi a kanta da danta Abdulazeez Ganduje ya shigar gaban hukumar.

Rahotanni sun ce Abdulazeez din ya shigar da korafi ne gaban hukumar EFCC a game da dambarwar sayen filaye, wanda mahaifiyarsa ta ki mutunta yarjejeniya.

Yanzu haka dan ya tsere zuwa wata kasar waje bayan da ya shigar da korafin.

Jaridar ‘Daily Trust’ ta ruwaito cewa an kama mai dakin gwamnan na jihar Kano ce bayan da ta yi watsi da gayyatar da EFCC ta yi mata tun da farko.

Bayan da aka gama yi mata tambayoyi ne ta koma Kano daga Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *