Kano: Babbar kotu ta umarci Ganduje ya biya Jaafar Jafaar N800,000 ko kuma…

Babbar kotun jihar Kano bisa alkalancin Justice S.B Namalam a ranar Litinin ta bukaci gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya biya mai jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar N800,000 bisa kashe-kashen kudaden da ya janyo ma sa na kotu sanadiyyar rikicin bidiyon dala.

Alkalin ya ce kotu ba za ta saurari Ganduje ba matsawar bai biya shi N800,000 ba kafin zagayowar ranar da kotu zata ci gaba da sauraron karar kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Lauyar Ganduje, Lydia Oyewo ta bai wa kotu hakuri kuma ta yi alkawarin tattaunawa da Ganduje don biyan kudin kamar yadda alkalin ya bayar da umarni tun ranar 6 ga watan Augustan 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *