Hukumar NFF ta gayyaci Isma’ila Mabo Lagos

Hukumar Kwallon kafar Najeriya ta nemi gafarar tsohon mai horar da Yan wasan ta na kungiyar mata ta Super Falcons, wato Ismaila Mabo saboda kuskuren da aka samu wajen kasa gayyatar sa wajen bikin karramawar da aka yiwa kungiyar sa a watan jiya.


Sakatare Janar na Hukumar Dr Sanusi Mohammed yace tabbas an samu kuskure wajen rashin halartar Mabo wajen bikin da suka yi, kuma ya kira shi domin neman afuwar sa dangane da lamarin.


Mohammed yace bayan sun baiwa Mabo hakuri, sun kuma gayyace shi zuwa Lagos domin halartar karawar da za’a yi tsakanin kungiyar kwallon kafar mata ta ‘Yan kasa da shekaru 20 da ake kira Falconets da takwarar ta ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniyar da za’ayi a shekarar 2022 a kasar Costa Rica.


RFI Hausa ta tintibi Mabo wanda ya tabbatar da samun kira daga Sakataren Hukumar kwallon kafar Dr Mohammed da kuma mataimakin shugaban ta Shehu Dikko.


Tsohon mai horar da ‘Yan wasan yace yanzu haka yana jiran tikitin sa na zuwa birnin Lagos domin halartar karawar da za’ayi gobe tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.


Rashin halartar Mabo wajen bikin karramar kungiyar sa da akayi a Lagos ya haifar da suka daga ciki da wajen Najeriya, yayin da Hukumar kwallon kafar tace kuskure ne ya haifar da matsalar.


Wannan ya sa RFI Hausa tayi hira ta musamman da Ismaila Mabo da kuma wasu masu ruwa da tsaki akan harkar kwallon kafar Najeriya, cikin su harda tsohon Sakatare Janar Sani Ahmed Toro wadanda suka bayyana bacin ran su da lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *