Gwamnatin Kano ta yi martani kan batun kame matar gwamna, Hajiya Hafsat Ganduje

Gwamnatin Jihar Kano ta mayar da martani kan rahotannin da ke cewa hukumar EFCC ta cafke matar Gwamna Abdullahi Ganduje, Farfesa Hafsat Ganduje, tana mai cewa labarai ne kawai wadanda ‘yan adawa ke daukar nauyin ta.

A cewar wata sanarwa, Kwamishinan Yada Labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya nuna nadama kan jita-jitar, inda ya kara da cewa ba za a iya bin diddigin labarin da ba shi da tushe daga wata tushe mai kyauta ba kamar dai hukumar EFCC kanta.

Ya bayyana cewa abin takaici, an yada labaran karya a kafafen sada zumunta ba tare da tabbatarwa daga gwamnati ko hukumar hana almundahanar ba, SaharaReporter ta ruwaito.

Garba ya ce:

“Ba a kama matar gwamnan ko aka tsare ta ba kuma a halin yanzu tana nan tana sauke nauyin da ke kanta.”

Kwamishinan ya yi kira ga mutanen kirki na jihar da su yi watsi da jita-jitar, inda ya bukace su da su kwantar da hankalinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *