Gwamnatin Buhari za ta fara biyan daliban digiri da NCE kudin kashewa

Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan N75,000 a matsayin alawus-alawus na kowane semester ga daliban da ke karatun digiri a fannin Ilimi a jami’o’in gwamnati a Najeriya, Punch ta ruwaito.

Hakanan, daliban NCE za su karbi N50,000 a matsayin alawus na kowane semester a wani kokarin gwamnati don jawo hankalin samar da kwararrun malaman makaranta kamar yadda Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya yi alkawari shekaran da ya gabata.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya sanar da hakan a ranar Talata 5 ga watan Oktoba, a bikin ranar malamai ta duniya da aka gudanar a Eagle Square da ke babban birnin tarayya Abuja.

Adamu, wanda Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Sonny Echono ya karanta jawabinsa a taron, ya ce ma’aikatarsa za ta hada kai da gwamnatocin jihohi don tabbatar da samar da aikin yi ga daliban kai tsaye kan kammala karatun.

Ya ce:

“Daliban digiri na B.Ed/B.A.Ed/ BSc.Ed a cibiyoyin Gwamnati za su karbi alawus na N75,000.00 a kowane semester yayin da daliban NCE za su sami N50,000.00 a matsayin alawus a kowane semester.

“Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta nemo hanyar da gwamnatocin jihohi za su iya ba da aikin yi ga wadanda suka kammala NCE a matakin Ilimi na farko.”

4 Replies to “Gwamnatin Buhari za ta fara biyan daliban digiri da NCE kudin kashewa”

  1. There are strategic implications:
    1. Would the modalities of disbursement be fair and void of corrupt practices?
    2. Will the promise be implement and kept going?
    3. What demand would the govt place on beneficiaries?
    4. Will it not be use as a blackmail or coercive by policy makers or any other immoral intruder?

Leave a Reply

Your email address will not be published.