Ferguson ya soki Solksjaer kan rashin fara wasa da Ronaldo

Sir Alex Ferguson ya caccaki matakin kocin Manchester United Ole Gunnar Solsjaer na rashin fara wasa Cristiano Ronaldo a karshen makon da ya gabata.

Caccakar tasa ta fito ne a wata fira tsakaninsa da shahararren dan damben martial arts, Khabib Nurmagomedov, wanda aka nada a bidiyo, kuma ta bayyana a dandalin sada zumunta.

A cikin minti na 57 ne aka sanya Ronaldo a wasan da Machester ta fafata  da Everton a ranar Asabar da aka tashi kunnen doki 1-1.

 Ferguson, wanda shine kocin da ya fi samun nasarori a tarihin Manchester United, kamata ya yi kowane mai horarwa ya fara wasa da manyan ‘yan wasansa, yana mai cewa abin da ya fado mai zuciya kenan a lokacin da ya fahimci ba a fara wasan da Ronaldo ba.

Wannan tsokaci na Ferguson zai ta’azzara matsin lamba a kan Solksjaer, duba da cewa ana ganin tsohon kocin na Manchester da kima.

One Reply to “Ferguson ya soki Solksjaer kan rashin fara wasa da Ronaldo”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *