Mutumin da ya yi zanen ɓatancin Annabi Muhammadu a Sweden ya yi ƙazamin hatsarin mota ya mutu

Mai hada fina-finan Cartoon, Lars Vilks dan kasar Swedin ya gwabza mummunan hatsari duk da ‘yan sanda sun ci gaba da ba shi tsaro tun shekarar 2007 da yaci zarafin mazon Allah, Muhammad SAW, sai ga shi ya halaka sanadin hatsarin mota.

Kamar yadda LIB ta ruwaito, tsohon mai shekaru 75 ya mutu tare da ‘yan sanda 2 da suke ba shi tsaro na musamman bayan motar su ta gwabza karo da wata babbar mota a ranar 3 ga watan Oktoba kamar yadda ‘yan sandan Swedin suka tabbatar wa da AFP.

LIB ta ruwaito yadda kakakin rundunar ‘yan sanda ya bayyana cewa: “Anyi bincike kamar yadda ake yi wa sauran hatsarorin kan hanya. Saboda har ‘yan sandan da ke tsaron sa sun halaka kuma yanzu haka an samar da bangaren bincike na musamman akan lamarin.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *