Mayakan Boko Haram sun mamaye garuruwa da dama a jihar Niger, inda suka raba wa mutane kudi suna daukansu a matsayin mayaka domin su taya su yaki da gwamnati, jami’in karamar hukuma da jiha ya shaidawa Reuters.
Suleiman Chukuba, shugaban karamar hukumar Shiroro na jihar Niger ya ce a halin yanzu mayakan Boko Haram suna mazabu 8 cikin jimillar 25 da ke karamar hukumarsa.
“Ba a san adadin mayakan kungiyar Boko Haram da ke karamar hukumar Shiroro ba.”
Boko Haram wacce ke yaki da karatun boko ta fara kai hare-hare ne tun 2009 sannan daga bisani kungiyar ISWAP da ta balle daga Boko Haram ita ma ta fara kai harin.
Yakin ya kashe kimanin mutum 350,000, miliyoyin mutane kuma sun rasa muhallinsu a cewar kididigar Majalisar Dinkin Duniya.
Yawan mutanen da ke Shiroro ya kai 331,000 a fadin kasa kilomita 4,7000 a cewar sashin gwamnatin jihar Niger.
Kwamishinan watsa labarai na jihar Niger Muhammad Sani Idris ya ce mayakan wadanda da farko ake zargin yan bindiga ne sun fara shigowa jihar. Amma Idris ya ce gwamnatin jihar da jami’an tsaro suna taka musu birki.
Muna yin duk abin da ya kama a matsayin mu na jihar, in ji shi. Kuma zamu cigaba da hadin kai tare da jami’an tsaro da ‘yan banga.
Rundunar sojojin Nigeria, a watan da ta gabata ta ce kimanin mayakan Boko Haram 6000 ne suka mika wuya.
Chukuba ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta turo karin sojoji yankin domin su yaki yan ta’addan.