Mahaifin kakakin majalisar Zamfara ya mutu a hannun ‘yan bindiga

A Najeriya, mahaifin kakakin Majalisar jihar Zamfara Nasiru Muazu Magarya, ya rasu a hannun ‘yan bindiga dake garkuwa da shi sakamakon bugun zuciya.

Babban dan uwan ​​marigayin, Malam Dahiru Saraki Magarya, ya tatabbatar da mutuwar Alhaji Muazu Abubakar, a wata hira da jaridar Buleprint.

Makonnin takwas da suka gabata aka yi garkuwa da Abubakar tare da mai dakinsa dauke da jariri mai makonni uku, da Malam Magarya da kuma wasu mutum biyu.

Kogi

A wani labarin kuma, tsohon shugaban Kwalejin Ilimi ta Jihar Kogi da ke Kabba, Julius Oshadumo, wanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi makwanni biyu da suka gabata, ya mutu a rikicin da ya barke tsakanin masu garkuwa da shi da jami’an tsaro, yayin da ake kokarin aikin ceton sa.

An yi garkuwa da jimi’in ne makonni biyu da suka gabata lokacin da wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai hari kan cocin ECWA da ke yankin Okedayo a Kabba ta Jihar Kogi, inda aka kashe mutum daya sannan aka raunata wasu masu ibada.

Leave a Reply

Your email address will not be published.