Fashewa ta hallaka mutane da dama a harabar wani masallacin Kabul

Wani fashewa a wajen wani masallaci a Kabul babban birnin Afghanistan ya kashe “fararen hula da dama” a wannan Lahadi.

Ta shafinsa na Twitter, Kakakin gwamnatin Taliban Zabihullah Mujahid ya bayyana Fashewar da ta auku kusa da kofar Masallacin Idi Gah da ke Kabul.

Ana gudanar da bikin addu’ar mahaifiyar Mujahid, wacce ta rasu a makon da ya gabata, a masallacin lokacin da lamarin ya auku, bikin addu’ar da tun a yammacin Asabar kakakin ya sanar da shafukan sada zumunta, tare da gayyatar ‘yan uwa da abokai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *