Duka Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun maka Gwamnatin Buhari a gaban kotun koli

Manyan lauyoyin gwamnatocin jihohi sun shigar da kara a kotun koli, suna kalubalantar doka mai cin gashinta ta 10 da Muhammadu Buhari ya kawo.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa jihohi suna neman kotu ta raba gardama a kan hallacin wannan doka da ta ba majalisa da kotun jihohi gashin kansu.

Gwamnatocin jihohin suna ganin cewa gwamnoni ya kamata su rika daukar dawainiyar kotunansu.

Gwamnoni sun yi imani cewa nauyin gwamnatin tarayya ne ta dauki hidimar albashi da sauran hakkokin manyan kotun tarayya, na shari’a da na daukaka kara.

Suna cewa dokar ta saba wa sassa na 6(5), 81(3) da layi na 21(3) na kundin tsarin mulkin kasa.

Rahoton da aka fitar dazu yace gwamnoni suna ikirarin dokar mai cikakkenn iko da shugaban kasa ya kawo ta ci karo da kundin tsarin mulki da dokar kasa.

Doka ta #10 ta ba Akanta-Janar damar ya cire kason kotunan jihohi daga kudin gwamnatin tarayya, ya tura masu rabonsu kai-tsaye ta majalisar shari’a, NJC.

Jaridar ta rahoto cewa gwamnatin tarayya ta bakin AGF ta maida martani a kotu, tana cewa aikinta ne ta biya Alkalai duk wasu albashi da alawus din aikinsu. Ministan shari’a, Abubakar Malami yace ba daidai bane gwamnonin jihohi su nemi gwamnatin tarayya ta biya su kudin da ta kashe a kan kotun da ke jihohinsu.

“Tun Mayun 1999, gwamnatin tarayya take daukar nauyin bangaren shari’a kamar yadda sashe na 84 na kudin tsarin mulki ya tanada.” – Abubakar Malami.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *