Wasu ma’aikatan asibitin a kasar Amurka sun zabi kora daga bakin aikinsu mai makon ayi masu allaurar rigakafin annobar korona saboda shakku da suke da ita.
Jennifer Bridges tana ƙaunar aikinta na jinya a Asibitin Methodist na Houston, inda ta yi aiki na tsawon shekaru takwas, amma ta zaɓi a kore ta maimakon yin allurar rigakafin COVID-19, ta yi imanin cewa allurar rigakafin ta fi barazana fiye da kwayar cutar.
Bridges na daya daga cikin ma’aikata kusan 150 da aka kora ko suka yi murabus maimakon amincewa da tsarin Methodist, dake zama na farko a Amurka da ya tilasta yin rigakafi.
Inda Kimanin wasu ma’aikata dubu 25,000 suka bi tsarin asibitin wajen karban allurar.