‘Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a jihar Neja

Wani rahoton gidan talbijin na AIT ya kawo cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe sojoji biyu a wani hari da aka kai garin Kagara da fadar Sarkin, a jihar Neja.

Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a garin Minna, babbar birnin jihar, jim kadan bayan ya ziyarci sojoji goma sha biyu da suka jikkata wadanda ke karbar magani a asibitin Ibrahim Badamasi Babangida.

Gwamnan ya kuma ce wasu daga cikin sojojin da suka jikkata suna samun kulawar likitoci a wani asibiti da ke Kaduna, sashin Hausa na BBC ya kuma ruwaito.

Gwamnan a cikin wata sanarwa daga Babbar Sakatariyar Yada Labarai, Mary Berje, ya ce babu takamaiman adadin wadanda suka mutu.

Gwamnan ya nuna damuwarsa game da karuwar ‘yan fashi da yadda suke tsarawa da aiwatar da hare-hare kan garuruwa.

Don haka ya umarci mutane da su kasance masu taka tsantsan game da tsaro tare da bayar da rahoton duk wani motsi da basu aminta da shi ba. Gwamna Bello ya kuma nuna damuwa game da wasu garuruwa da ke dauke da ‘yan fashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *