Sojoji sun bayyana abin da ya sa suka buda wuta ga masu kama kifi, suka aika mutum 20 barzahu

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Hedikwatar tsaro ta Najeriya tayi karin haske game da kashe wasu masu su da sojoji suka yi a jihar Borno.

Hedikwatar tsaro na kasar watau DHQ tace ta hallaka ‘yan ta’addan ISWAP ne da suka fake da kamun kifi, suna yin ta’adi a yankin tafkin Chadi. A wani jawabi da hedikwatar ta fitar ta bakin darektan harkokin yada labarai, Birgediya-Janar Benard Onyeuko, ta bayyana ainihin abin da ya faru.

Birgediya-Janar Benard Onyeuko yace sojoji sun gano ‘yan ta’addan suna yin shigar masunta, su dauki wasu kaya a cikin jiragen ruwa a gabar rafin.

Jami’in sojojin kasar yace sun gano wadannan mutane ba kama kifi suke yi ba, suna ta jigilar wasu kaya da ba a san menene ba, suna yin gaba da su.

Jaridar ta rahoto Janar Benard Onyeuko yana cewa har yanzu ba a halasta kamun kifi a yankin ba.

“Hankalin hedikwatar tsaro ya zo ga wani karkataccen labarai da yake yawo a kafafen sadarwa na zamani cewa OPHK ta kashe masunta 20 da ke kiwon kifi a wani hari ta jirgin sama a Kwatan Daban Masara a ranar Lahadi, 26 ga watan Satumba, 2021, a kusa da yankin tafkin Chadi a Arewa maso gabashin Najeriya.”

Akasin abin da aka rahoto, sojoji sun gano ‘yan ta’addan ISWAP ne, ba masunta ba, sai aka kai hari.”

Sojoji sun samu bayanan sirri tsakanin Agusta da Satumban 2021 cewa ‘yan ta’addan Islamic State West Africa Province (ISWAP) sun yi kaca-kaca da yankin.

Daga nan sai aka gudanar da bincike na musamman a yankin, aka tabbatar da cewa ‘yan ta’adda suna yin lambo, bayan nan sai sojojin sama suka kai masu hari.

Leave a Reply

Your email address will not be published.