Qatar na zaben ‘yan majalisar Shura karon farko

‘Yan kasar Qatar sun fara kada kuri’a a zaben’ yan majalisun Shura a karon farko a wannan Asabar, wanda ke matsayin wata alama ta dimokuradiyya ko da yake masu sharhi na ganin ba za ta kai ga sauya mulki daga dangin dake mulki ba.

‘Yan majalisun shuru 30 za’a zaba cikin wakilai 45, wanda a baya sarkin Qatar, Sheikh Tamim Bin Hamad Al Thani ke nadawa.

Masu lura da al’amura sun ce kudin tsarin mulkin kasar na shekarar 2004 ya tanada zaben amma aka jinkirtawa sai kuma a wannan karo da kasar ke shirin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *