Hotunan wani mutum da ya auri tukunyarsa ta dafa shinkafa ya ɗauki hankulan mutane

Wani mutum dan asalin kasar Indonesia ya janyo cece-kuce bayan ya bayyana yadda shagalin auren sa da tukunyar girkin lantarkin sa ya kasance.

Kamar yadda ya wallafa hotunan bikin, ya na sanye ne da fararen kaya na alfarma yayin da tukunyar take lullube da mayafi irin na amare kamar yadda LIB ta ruwaito.

Anam ya kambama sabuwar amaryar ta sa Mutumin mai suna Khoirul Anam cikin shauki da tsananin farin ciki ya yi wallafar ya na kambama amaryar ta sa inda ya sa “Sabuwar amarya”. Kamar yadda ya wallafa: “Fara ce tas kuma ba ta da yawan magana ga shi ta kware a girki.”

Khoirul Anam ya wallafa hotunan a shafin sa na Facebook inda ya bayyana cewa an daura auren sa da tukunyar girkin lantarkin tun ranar 20 ga watan Satumba kamar yadda LIB ta ruwaito. 

Hotunan sun yi yawo kwarai a kafafen sada zumuntar zamani inda mutane daban-daban su ka yi ta tsokaci iri-iri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *