Buhari ya bada umurnin a buɗe wa ‘yan Nigeria Twitter, amma da sharaɗi

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Juma’a, ya ce ya bada umurnin a dage dakatarwar da aka yi wa shafin Twitter a Nigeria tun watan Yunin 2021.

The Punch ta ruwaito cewa Buhari ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi wa ‘yan Nigeria na ranar bikin samun ‘yancin kasa karo na 61.

Ya bayyana cewa kafafen sada zumunta na da amfani amma ya yi koka kan yadda wasu ke amfani da kafar don shirya muggan ayyuka da watsa labaran karya da kabilanci da tada rikicin addini.

Shugaban kasar ya ce: “Kafar sada zumunta na da amfani sosai kuma ya bawa miliyoyin yan Nigeria daman yin zumunci da kasuwanci da samun labarai da wasu bayanai.

Amma, abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun nuna ba wai kafa bane kawai na watsa bayanai.

“Wasu na amfani da shi ta hanyar da bai dace ba don shiryawa da aikata miyagun ayyuka, watsa labaran karya da kyamatan juna saboda banbancin kabila da addini.

“Don magance wannan matsalolin, gwamnatin tarayya ta dakatar da Twitter a Nigeria a ranar 5 ga watan Yunin 2021 don bawa gwamnati damar daukan matakan magance wadannan kallubalen.

“Bayan dakatar da shafin Twitter, kamfanin Twitter ya tuntubi gwamnatin Nigeria don warware matsalar. Daga bisani, na kafa kwamitin shugaban kasa don tattaunawa da Twitter don warware matsalar.

“Kwamitin ya gana da Twitter don duba wasu abubuwa masu muhimmanci. Abubuwan sune tsaron kasa da hadin kan kasa; Rajitsa, Bude Ofishi a Nigeria da wakilci; Haraji; Warware matsaloli; Tallata abubuwan gida Nigeria.

“Bayan tattaunawa mai tsawo, an warware lamuran kuma na bada umurnin a dage dakatarwar da aka yi wa Twitter amma idan an cike sharrudan domin bawa yan kasarmu damar cigaba da yin amfani da shafin don kasuwanci da abubuwa nagari.

“A matsayin mu na kasa, za mu tabbatar cewa kamfanonin sadarwar zamani na amfani da kafarsu don inganta rayuwarmu, girmama ‘yancin Nigeria, al’adunta da tsaro a yanar gizo.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *