Ƴan jaridan da suke kiran ƴan bindiga ƴan ta’adda ne asalin ƴan ta’addan

Sheikh Gumi, babban malamin addinin musuluncin nan na Kaduna ya ce ‘yan jaridar da suke kiran ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ne asalin ‘yan ta’addan.

Kamar yadda Arise News ta ruwaito, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan Talabijin din Arise ta yi da shi, ya ce akwai buƙatar a rungumi ‘yan bindiga a al’umma.

Daya daga cikin mai gabatar da shirin ya bayyana yadda ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda suke yayin da ya tambayi malamin abinda suke so kafin su zubar da makaman su.

Yayin da Gumi yake amsa tambayar sa, ya ce ‘Yan jarida ne ‘yan ta’addan kuma bai dace su kira ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ba.

A cewarsa, yanzu haka a shirye ‘yan bindiga suke da su zubar da makaman su, amma duk lokacin da su ka ji ana yada labarai akan su, ana kiran su da ‘yan ta’adda, sai su hassala su ci gaba da gashi bisa ruwayar News Ngr.

A cewar Gumi, matsawar ana so ‘yan bindiga su dena addabar al’umma su dena kashe-kashe, wajibi ne a rungume su a kyautata mu su kamar yadda ake yi wa sauran ‘yan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.