Tsadar kayan abinci: Buhari ya ɗora alhakin kan ‘yan kasuwa, ya ce suna boye kaya don samun kazamar riba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ‘yan kasuwa za a zarga a kan hauhawar farashin kayan abinci a kasar.

A yayin jawabinsa na kasa baki daya don murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yancin kai a ranar Juma’a, 1 ga Oktoba, shugaban kasar ya ce ‘yan kasuwa sun haifar da karancin abinci ta hanyar boye kayayyaki don samun riba mai yawa.

Shugaban na Najeriya ya bayyana cewa:

“Abin takaici ne, yayin da adadin abincin da ake nomawa a kasar ya ƙaru, farashin abinci yana ta hauhawa saboda boye wadannan kayan abinci da ‘yan kasuwa ke yi don cin riba.”

Don magance wannan matsalar, Shugaba Buhari ya umarci Ma’aikatar Noma da Raya Karkara da ta gyara Hukumar Kula da adana Abinci ta Kasa.

Ma’aikatar za ta kuma hada gwiwa da hukumomin tsaro, Hukumar Kula da Kayan Masarufi da kuma Majalisar Dokokin Tarayya don nemo mafita ta dindindin ga wadannan ayyukan na boye abinci da shugaban kasar ya bayyana a matsayin masu kawo cikas da rashin kishin kasa.

A cewar shugaban na Najeriya, bangaren aikin gona ya kasance mabuɗin ci gaban tattalin arzikin ƙasar.

Ya kara da cewa don ci gaba da inganta noman abinci, an kammala sabbin madatsun ruwa da dama yayin da wasu hukumomin raya Kogi, musamman domin taimaka wa harkar noman rani.

ba.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.