Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci Gwamnonin Kudanci da Arewacin Najeriya da suyi watsi da sabanin dake tsakanin su domin su cigaba da zama tsintsiya Madaurin ki daya don ciyar da Kasar gaba.
Gwamnan yayi wannan Kiran ne lokacin da yake jawabi wajen bikin Cikar Najeriya shekaru 61 da samun yancin kai a Sani Abacha Stadium dake Kofar Mata.
Ya kara da cewa gwamnan ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa aiki da suke ba dare ba rana wajen tabbatar da tsaro a fadin Jihar Kano inda yace Gwamnatin sa zata cigaba da nemo hanyoyi na zamani domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma.
Taron ya sami halartar mataimakin Gwamna, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da Sarakunan Kano masu daraja ta daya da shugabannin hukumomin tsaro da yan majalisu da shugabannin yan kasuwa da kuma daukacin Jami’an Gwamnati.