Kotun Faransa ta aike da Nicolas Sarkozy gidan yari na shekara guda

Kotun a birni Paris da ke  Faransa ta zartas da hukuncin dauri ga tsohon Shugaban kasar Nicolas Sarkozy da ake tuhuma da laifuka da suka hada kashe kudin da ya wuce kima yayin yakin neman zabe, almundahana da kuma halasta kudin haram.

Kotun ta birnin Paris ta aike da Sarkozy gidan yarin na shekara guda ne bayan samunsa da laifuffukan da ake tuhumarsa ciki har da kashe kudin da suka wuce kima yayin yakin neman zaben shekarar 2012.

Hukuncin wanda kotu ta zartas ba tare da bayyanar Sarkozy gabanta ba, wasu bayanai sun ce dai dai lokacin da kotun ke hukuncin shi kuwa Sarkozy na halartar wani taron ganawa da jama’a na daban a cikin kasar.

A cewar Caroline Viguier wacce ta shugabanci zaman kotun na yau ,lura da cewa Nicolas Sarkozy ya shugabanci kasar Faransa bayan lashe zabukan shekarar 2007 wanda kuma ke da masaniya dangane da dokokin kasar a sha’anin yakin neman zabe da kudadden da ya dace jam’iyyoyi su kashe a kai.

A watan Maris, tsohon Shugaban kasar ta Faransa Nicoals Sarkozy ya kasance shugaba na farko da kotu ta zartaswa hukunci daurin shekara daya a kurkuku, bayan samun sa da laifin rashawa da kokarin  mika na goro ga wani alkalin kasar.

Sai dai Lauyan Sarkozy, Therry Herzog ya ce su na shirye don ganin kotu ta soke wannan hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *